in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Burundi ta cimma matsayin rage adadin yara masu fama da tamowa
2014-07-03 14:21:34 cri

Kasar Burundi ta cimma wani matsayin rage adadin yara masu fama da rashin abinci mai gina jiki a wajen yara 'yan kasa da shekaru biyar tun babban taron kasa na farko kan tsaron abinci da ciyarwa tare da taimakon kungiyar abinci ta duniya (PAM) a cikin watan Disamban shekarar 2011, in ji wakilin PAM dake kasar Burundi, mista Bienvenu Djossa a ranar Laraba a wata hirarsa tare da kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

Mista Djossa ya yi furucin a lokacin dandalin horaswa kan ciyarwa a kasar Burundi da ma'aikatar kiwon lafiyta ta kasar Burundi ta shirya tare da taimakon PAM, inda jami'in ya bayyana cewa, jin dadinmu a yanzu shi ne yadda mutanen kasar Burundi na mai da hankali sosai kan babbar illar rashin abinci mai gina jiki ke janyowa bil adama, da ma matsalar karancin abinci a cikin kasa.

Haka kuma mista Djossa ya nuna yabo kan kokarin da gwamnatin kasar da kungiyoyin ba da tallafi suke yi a wannan fanni. Hakika muna dogaro da taimakon kafofin watsa labarai wajen isar da sako ga al'ummar kasa baki daya domin su gane muhimmancin cin abinci, abin da ya kamata su ci, sannan kuma a wane lokaci, ta yadda adadin rashin cin abinci mai gina jiki zai rika cigaba da raguwa a kasar Burundi.

Wasu alkaluman binciken yawan jama'a da kiwon lafiyar (EDS) na shekarar 2008 sun nuna cewa, matsakaicin adadi game da rashin abinci mai gina jiki wajen yaran Burundi 'yan kasa da shekaru biyar ya cimma kashi 58 cikin 100. Amma a cikin watan Mayun da ya gabata, sabbin alkaluman binciken da aka gudanar sun nuna raguwar wannan adadin da kashi 48 cikin 100. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China