Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir da tsohon mataimakinsa Riek Machar sun rattaba hannu a kan wata yarjejeniya sulhu ta dakatar da fadan da ake tafkawa a kasar.
An dai samu damar tattaunawa ne tsakanin shugaban kasar da tsohon mataimakinsa a karkashin shiga tsakani na IGAD, kuma an sa hannun kan yarjejeniyar ne domin kawo karshen yakin da ya barke a watan Disambar shekarar 2013.
Kundin yarjejeniyar ya bayar da tabbacin girka gwamnatin rikon kwarya ta hadin kan kasa tare da kafa hukumomi na wucin gadi na shari'a da kuma matakai na sa ido a kan lamurra.
Firaministan kasar Ethiopia Hailemariam Dessalegn ya bukaci sassan biyu da su girmama yarjejeniyar da suka rattaba hannu a kai.
Wakili na musamman na shugaban kungiyar IGAD a Sudan ta Kudu Eyoum Mesfin ya ce, za'a kammala tattaunawa a kan yarjejeniyar lumana tsakanin sassan biyu a ranar 20 ga watan Fabarairu da muke ciki domin girka cikakken tsari na zaman lafiya, ko kafin ranar 5 ga watan Maris. (Suwaiba)