in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yanayin tsaron Sahel ya kyautata, in ji ministan tsaron Nijar
2015-01-27 10:12:32 cri

Ministan tsaro na kasar Niger Karidjo Mamadou ya jaddada cewa, yanayin tsaro a yankin Sahel na nahiyar yana da kyau a yanzu, kuma ana kokarin kammala shirin da ake na kawar da duk wata barazanar ta'addanci.

Karidjo Mamadou ya fadi hakan ne a lokacin da yake jawabi ga manema labarai sakamakon ganawar shi da babban hafsan sojin kasar Algeriya laftanar janar Ahmad Kaid Saleh a Algiers, babban birnin kasar.

Ya ce, hadin gwiwwar soji tsakanin kasashen biyu ya yi nasara, kuma makwabtan biyu sun tattauna duk batutuwa da suka shafi tsaro da ya addabi yankin, musamman ma a kwamitin sojin hadin gwiwwa na kasashen yankin Sahel CEMOC, da kuma shirin da ake na hadin gwiwwarsu.

Wannan kwamitin dai na sojin hadin gwiwwa ne da kasashen Algeriya, Niger, Mali da Mauritaniya suka kafa a shekara ta 2010 domin yakar ta'addancin da sauran laifuffuka a yankin. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China