Kwamitin tsaro na MDD ya nuna damuwar sa a game da kungiyoyin 'yan ta'adda dake gudanar da ayyukansu a yankin Sahel, wadanda ke haddasa ta'asa ta tashin hankali, da saffarar makamai da aikata laifuka na kasa da kasa, tare da fataucin muggan kwayoyi a wani lokaci kuma har da aikata ta'addanci.
Kwamitin tsaron ya yi nuni da matakai da yankuna da kasashen duniya za su iya dauka domin murkushe kungiyoyin 'yan ta'adda.
A cikin wata sanarwa kwamitin tsaron mai mambobi kasashe 15, ya yi allah wadai da hare-hare na ta'addanci da aka kai a yankin na Sahel a kwanan nan.
Kwamitin tsaron ya yi maraba da wata sanarwa ta kafa kungiyar kasashe 5 ta yankin Sahel ko kuma G5, wacce wata sabuwar kungiya ce da kasashen Sahel tsantsa, suka kafa wacce ta kunshi Burkina Faso, Chadi, Mali, Mauritania da Niger a ranar 16 ga watan Fabrairun wannan shekarar.
Kwamitin tsaron ya ce, ita wannan kungiyar ta shirya kafa wata kungiya da za ta biyo baya a birnin New York, wacce za ta kunshi mambobi na din din din na kungiyar ta G5, wacce za ta kunshi sauran kasashe daga yankin na Sahel.
Kwamitin tsaron ya yi kira a kan kasashen duniya da su bayar da taimako wajen kafa cibiyoyi na yankuna wadanda za su dinga gudanar da sintiri na tsaro tare da musayar bayanai. (Suwaiba)