in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana ta alkawarta bunkasa wasannin nakasassu
2014-12-03 10:59:44 cri

Kasar Ghana ta shirya gudanar da gasar wasannin motsa jiki ajin nakasassu, a wani mataki na bunkasa harkokin motsa jiki domin al'ummar kasar masu fama da nakasa.

Rahotanni daga ma'aikatar wasannin kasar dai sun nuna cewa, za a gudanar da gasar ne ta wannan karo daga ranar 11 zuwa 13 ga watan Disamabar nan a birnin Accra.

A cewar babban sakataren hukumar wasannin nakasassu ta kasar Ignatius Elletey, gasar za kuma ta ba da damar zakulo 'yan wasa masu basira maza da mata, wadanda za su wakilci kasar a gasar Olympic ta nakasassu a shekarar 2016 dake tafe.

Ana dai sa ran 'yan wasa sama da 200, za su halarci wannan gasa daga sassan kasar daban daban. Gasar da ta kunshi wasannin goalball, da kwallon tebur, da kwallom kwando, da wasan taekwondo, da kwallon kafar nakasassu da kuma tennis.

A baya dai wannan aji na 'yan wasan kasar ta Ghana sun samu nasarori masu yawa a gasannin kasa da kasa da suka halarta, yayin da kuma mahukuntan kasar ke fatan 'yan wasan da su kara ciyowa kasar karin lambobin yabo a nan gaba. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China