Gwamnatin kasar Ghana ta sanar a ranar Talata da niyyar kyautata matsakaicin albashi a yini guda na kasa da kashi 16,7 cikin 100. Ministan kwagadon kasar Ghana, Haruna Iddrisu, ya gaya wa manema labarai cewa, sabon albashin ya fara aiki tun daga ranar daya ga watan Janairun shekarar 2015. An dauki matakin a ranar Talata, bayan mako guda ana tattaunawa a cikin wani kwamitin bangarori uku na kasa (NTC) dake kunshe da wakilan gwamnati, kungiyoyin kwadago da kungiyoyin shugabannin kamfanonin kasar Ghana (GEA). (Maman Ada)