Hukumar NBC mai kula da ayyukan kafofin watsa labarai a Najeriya, ta ce, za ta hukunta duk wata kafar watsa labarai, da ta fidda bayanai da ka iya tunzura jama'a.
Wata sanarwa da ofishin babban daraktan hukumar Emeka Mba ya fitar, ta ce, NBC ta lura da yadda wasu kafofin watsa labarai, ke yada bayanai da suka shabawa muradun wanzar da zaman lafiya, da burin da ake da shi na gudanar zaben kasar dake tafe lami lafiya.
Mr. Mba ya ce, akwai bukatar kafofin watsa labarai su hada kai waje guda, wajen tabbatar da ba da tasu gudummawa, a fannin gudanar zaben dake karatowa cikin kyakkyawan yanayi.
Ya ce, ya zama wajibi a saita shirye-shirye, musamman na siyasa, ta yadda za su dace da dokokin kasa, ba tare kuma da kunsa kalaman batanci, ko cin zarafin wani ba, matakin da a cewar Mba zai taimaka matuka, wajen kammalar zaben na wannan wata cikin kwanciyar yanayi. (Saminu)