Ministan ilmi na Nigeria Ibrahim Shekarau ya ce, kananan makarantun firamare na gwamnati da masu zaman kansu za su ci gaba da kasancewa a bude a lokacin zabe.
Ministan wanda ya bayyana hakan a yayin da yake yi wa 'yan jarida jawabi bayan ya kammala wani taro da kwamishinoni na ilmi dake jihohi 36 na Nigeria.
Ministan ya ce, babu kwararan dalilai da za su sa a kulle makarantun, musamman da yake gwamnatin Nigeria ta shirya daukar matakai na samar da kariya ga makarantun a lokacin zaben.
Shekarau ya jaddada cewar, ya kamata iyaye su kwantar da hankulansu tare da yin biris da dukanin jita-jita domin zaben da za'a yi shi cikin kwanciyar hankali da lumana ba tare da wani tashin hankali ba, ko kuma barazanar zubar da jini.
Ministan ya ce, idan iyaye sun tura yaransu zuwa makaranta, amanar yaran tana ga hannun hukumomin makaranta, kuma gwamnatin Nijeriya ta kuduri aniya ta samar da kariyar da ake bukata.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta Nigeriya ta kebe ranar 14 da 28 ga watan Fabarairu domin gudanar da zaben shugaban kasa da na gwamnoni. (Suwaiba)