in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi kashedin aukuwar mummunar makoma sakamakon rikicin dake addabar Libiya
2014-12-24 10:05:41 cri

Wani sabon rahoto da tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a Libiya, da hadin gwiwar ofishin kiyaye hakkokin bil'adama na MDDr suka fitar, ta yi kashedin cewa, fadace-fadace dake ci gaba da aukuwa a Libiya, na iya haifar da mummunan sakamako ga kasar.

Rahoton ya ce, a baya bayan nan dakarun kasar masu dauke da makamai sun hallaka daruruwan fararen hula, tare da tilasawa wasu da dama kauracewa gidajensu. Har wa yau rahoton ya ce, akwai shaidu dake nuna yadda mayakan ke kaddamar da hare-hare kan fararen hula, da yin garkuwa da wasu, tare da barnata dukiyoyi ba ji ba gani.

Game da yankunan da rikicin ya fi kamari kuwa, rahoton ya lasafta yammacin Warshafana, da tsaunukan Nafusa, da kuma gabashin Benghazi, a matsayin wuraren da al'ummunsu suka fi fuskantar matsalolin karancin abinci, da ruwan sha, da rashin isassun magunguna, sakamakon karuwar tashe-tashen hankula.

Tawagar wanzar da zaman lafiyar ta UNSMIL ta ce, ta samu rahotannin dake nuna yadda wasu dakaru suka yi amfani da kayan kungiyar ba da agajin jin kai ta Red Crescent, suka kuma kai harin kunar bakin wake da motar kungiyar a birnin Benghazi.

Game da hakan ne wakilin musamman na babban magatakardar MDD a kasar ta Libiya Bernardino Leon, ya ja hankulan dukkanin bangarorin da rikicin siyasar kasar ya shafa, da su gaggauta dakatar da bude wuta ba tare da wani bata lokaci ba.

Dauki ba dadin da sassan kasar ta Libiya biyu ke yi tun bayan kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Muammar Gaddafi a shekarar 2011 dai, ya haifar da kafuwar gwamnatoci 2 dake adawa da juna. Lamarin da kawo yanzu ke dada jefa kasar cikin mawuyacin hali na tashe tsahen hankula. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China