Shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe ya ce, ayyukan kwangila tsakanin kasar Zimbabwe da kasar Sin suna taimakawa wajen zaburar da ci gaban kasar ta kudancin Afrika a fannonin kiwon lafiya da ilmi. Shugaba Mugabe wanda ya kawo ziyarar aiki a nan kasar Sin a watan Agusta, ya shaida wa wakilan majalisar dokokin cewar, gwamnatinsa ta kammala amsar lamuni na dalar Amurka miliyan 89 daga bankin shigi da fici na kasar Sin, China Exim Bank domin sayen injuna da kayayyaki na bunkasa lafiya wadanda suka hada da motocin dauko maras lafiya a cikin gaggawa da sauran kayayyaki na fannin lafiya.
Shugaban kasar ya ce, bankin na Exim zai taimaka kwarai wajen inganta bangaren kiwon lafiya a kasar ta Zimbabwe.
Bangaren kiwon lafiya na kasar na fuskantar matsaloli da suka hada da rashin kayayyakin aiki da manyan injuna da kuma asarar ma'aikata, ya zuwa kasashen ketare da rashin biyan albashi mai tsoka.
Ana shi bangaren, jakadan kasar Sin a Zimbabwe Lin Lin ya ce, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, kasar Sin ta bai wa kasar Zimbabwe bashi mai rahusa har kimanin dalar Amurka biliyan guda daga kafar Exim Bank, domin gudanar da ayyuka na gina kwalejin tsaro kasar da kuma wani aiki na samar da ruwan sha a Harare, tare da samar da kayayyaki da injunan da ake bukata a asibitoci da sauran ayyuka na ci gaba da suka hada da fadada filin jirgin sama na Victoria da kuma kara girman tashar samar da wutar lantarki a Kariba South ta kasar. (Suwaiba)