in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD za ta taimaka kan zaben a Burundi a shekara ta 2015
2014-05-07 11:57:09 cri

Wakili na musamman mai wakiltar babban sakataren MDD a kasar Burundi, Parfait Onanga Anyanga ya bayyana cewar, MDD a shirye take ta tallafa wa Burundi, wajen gudanar da zaben kasar na shekara ta 2015.

Shi dai Anyanga yana jawabi ne, a yayin da ya kammala ganawa da Mataimakin shugaban kasar Burundi na farko, Prosper Bazombanza a Bujumbura babban birnin kasar.

Anyanga ya ce, rahotanni na gwamnati, na nuni da cewar, ita dai MDD ta kasance tana mai nuna gamsuwa a game da halin tsaro na kasar Burundi.

Wakilin musamman na MDD ya baiwa hukumomin Burundi kwarin gwiwa domin su tababbatar da cewar, idan an yi zaben shekara ta 2015, kasar za ta zamanto cikin kwanciyar hankali da lumana. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China