in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An samu kyakkyawan sakamako a dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka
2014-12-11 10:15:24 cri

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Zhang Ming ya bayyana cewa, taron manyan jami'an dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC) karo na 10 da aka gudanar a birnin Pretoria na kasar a Afirka ta Kudu ya haifar da kyakkyawan sakamako a sassan nahiyar baki daya.

Zhang ya ce, tun lokacin da aka kaddamar da dandalin a shekara ta 2000, an yi nasarar fadada tare da inganta hanyoyin tafiyar da ayyukan dandalin, baya ga yadda dandalin ya kara karfafa bunkasa hadin gwiwar Sin da nahiyar ta Afirka.

Mataimakin ministan na Sin ya kuma bayyana cewa, hadin gwiwar sassan biyu ta kai ga samun karuwar cinikayya tsakanin Sin da Afirka, wadda ta kai dala biliyan 210 a shekara ta 2013, adadin da ya ninka na shekara ta 2000 sau 21.

Bugu da kari an samu karuwar harkokin zuba jari da hadadar kudi tsakanin sassn biyu, inda yawan jarin da Sin ta zuba kai tsaye a Afirka ya kai kimanin dala biliyan 30, yayin da rancen kasuwancin da Sin ta baiwa kasashen Afirka ya kai dala biliyan 50, baya ga hadin gwiwar ayyukan da ta kulla a baki dayan nahiyar.

A shekara mai zuwa ne dandalin na FOCAC zai yi bikin cikar sa shekaru 15 da kafuwa, inda kasar Sin ta bayyana shirinta na yin aiki tare da kasashen Afirka don tabbatar da samun nasarar taron ministocin dandalin tare da daga sabon matsayin hadin gwiwar Sin da Afirka gaba. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China