in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta cigaba da yin hadin gwiwa da Afrika, in ji jakadan kasar a Habasha
2014-01-16 10:14:06 cri

Kasar Sin za ta cigaba da hadin gwiwa cikin gaskiya tare da Afrika kuma za ta taimakawa nahiyar bunkasa tattalin arzikinta, in ji jakadan kasar Sin dake kasar Habasha a ranar Laraba.

Wata hira tare da manema labarai a ginin cibiyar tarayyar Afrika AU da wani kamfanin kasar Sin ya gina a babban birnin na kasar Habasha, jakada Xie Xiaoyan ya sake tunatar da cewa, hadin gwiwa da huldodin dake tsakanin Sin da Afrika na da tsawon shekaru masu tarin yawa. Mista Xie wanda shi ma wakilin kasar Sin a kungiyar tarayyar Afrika, ya bayyana cewa, Sin na fatan karfafa hadin gwiwa tare da Afrika da ma wasu karin kasashen dake nahiyar.

Da yake magana kan ziyarar firaminstan kasar Japan a nahiyar Afrika, jakada Xie ya bayyana cewa, firaminstan kasar Japan ya yi yunkurin kawo rudani da rikici tsakanin Sin, kasashe makwabtanta da wasu kasashe na yankunan duniya.

Jakada Xie ya nuna cewa, Afrika da jama'arta da suke da nisa da yankin Asiya, ya kamata su samu bayanai kan abubuwan da suka faru a lokacin da kasar Japan ta mamaye wasu kasashen Asiya da kuma sanin kunbiya kunbiyar da shugabannin Japan suke yi a halin yanzu.

A yayin da take cigaba da yin hadin gwiwa cikin gaskiya tare da Afrika, kasar Sin za ta cigaba da ba da tallafinta wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a nahiyar Afrika, in ji jakada Xie Xiaoyan. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China