in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kashe masu sha'awar kwallon kafa 22 a Masar yayin fito na fito da 'yan sanda
2015-02-09 10:40:56 cri

A kalla masu sha'awar kwallon kafar Masar 22 ne aka kashe a yayin da kimanin wasu 20 suka jikkata a ranar Lahadi a cikin wani fito na fito tare da 'yan sanda a birnin Alkahira, hedkwatar kasar Masar, a cewar kamfanin dillancin labarai na kasar Masar MENA.

Rikicin ya barke a yayin da magoya bayan kungiyar Zamalek, da kuma aka fi sani da "Chevaliers blancs" suka yi yunkurin shiga filin wasa na Air Defense Stadium dake birnin Alkahira domin kallon wasa tsakanin Zamalek da Enppi ba tare biyan ko dala ba.

Mutanen sun mutu dalilin rashin lumfashi bayan an tattake su, bayan kuma 'yan sanda sun yi amfani da barkonon tsofuwa domin tarwatsa su, a cewar wata sanarwa ta ma'aikatar cikin gida ta kasar. Amma kuma duk da wannan rikici da ya janyo asarar rayuka, an ci gaba da gudanar wasan har karshe.

A shekarar 2012, makamancin irin wannan rikici ya barke a wani filin wasan birnin Port Said, lamarin da ya janyo mutuwar mutane 73, da jikkata wasu daruruwan mutane a yayin taka leda tsakanin kungiyoyin Al-Masry da Al-Ahli. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China