Kwamitin tsaro na MDD ya yi suka da babbar murya game da ci gaban hare haren da 'yan kungiyar Boko Haram suke kaiwa, wadanda suka hada da na bayan bayan nan da suka kai wa sojojin kasar Chadi da aka tura domin hadin gwiwwa a kan iyakar kasashen Kamaru da Nigeriya.
Kusan mayakan 7000 ne aka ba da rahoton sun afkawa garin Fotokol dake da nisa daga arewacin Kamaru da kan iyaka da Nigeriya a safiyar ranar Laraban da ta gabata, abin da ya yi sanadiyar mutuwar sojojin Chadi 13 da raunata wassu da dama.
An yi bata kashi mai karfi tsakanin 'yan kungiyar da kuma sojojin hadin gwiwwa na Chadi da Kamaru. Fotokol dai ya fada hannun 'yan tsagerar, amma daga baya sojoji suka sake kwato shi 'yan awannin kadan da karbe shi. Kuma ana kyautata cewa, an hallaka 'yan tsagere sama da 300 lokacin gumurzun.
A cikin wata sanarwa da aka fitar wa manema labarai, kwamitin sulhun MDD ya lura da cewar, ramuwar gayyar harin da sojojin Chadin suka yi a kan mayakan na Boko Haram a Nigeriya, an yi shi ne bisa izini da amincewar gwamnatin tarayyar Nigeriya wanda yankinta ya kasance cikin 'yanci.
Kwamitin daga nan sai ya jaddada damuwarsa game da yanayin zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin yammacin da tsakiyar Afrika, sannna kwamitin ya yi kira ga yankunan da su inganta sojojinsu da kayayyakin aiki da tsari, yadda za su iya shawo kan matsalar kungiyar ta Boko Haram cikin sauri. (Fatimah)