in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
GDP a kasashen kudu da Sahara zai karu da kashi 5,5 cikin 100 bana, in ji IMF
2014-04-25 10:35:48 cri

Asusun kudin duniya IMF ya yi hasashen cigaban GDP a kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara zai gaggauta karuwa da kashi 5,5 cikin 100 a shekarar 2014, idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata dake kashi 4,9 cikin 100.

Shugabar sashen Afrika na asusun IMF, madam Antoinette Sayeh ta shaida wa 'yan jarida a ranar Alhamis a birnin Nairobi cewa, wannan karuwa za ta kara zuba jari a cikin bangarorin gine-gine da ma'adinai, kuma hakan zai bayyana hasashen kyautatuwar harkoki a cikin yawancin kasashen dake fitar da man fetur, da kuma cikin yawancin kasashen da ba su samun riba mai karfi, da kuma kasashe marasa karfi.

Amma kuma wannan hasashe yana dogara da yawacin haduran da aka rage idan aka kwatanta da na shekarun da suka gabata, in ji madam Sayeh a yayin bikin kaddamar da rahoton rabin shekara kan hasashen tattalin arzikin shiyya na IMF kan kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara a birnin Nairobi. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China