in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a gudanar da taron nazarin tattalin arzikin Afirka a Maputo
2014-05-29 09:59:12 cri

Asusun ba da lamuni na IMF da hadin gwiwar gwamnatin kasar Mozambique, sun shirya gudanar da wani taron nazari kan inganta bunkasuwar tattalin arzikin nahiyar Afirka a birnin Maputon kasar ta Mozambique.

Ana dai sa ran taron na yini biyu, zai mai da hankali kan nazartar kalubalen dake fuskantar yankunan dake kudu da hamadar Sahara, a daidai gabar da yankin ke samun habaka, tun bayan matsalar tattalin arzikin duniya da ta auku a shekarar 2008.

Wata sanarwa da IMF ya fitar ta rawaito babbar daraktan asusun Christine Lagarde, na cewa, cikin muhimman batutuwan da za a tattauna a kan su, hadda nazarin hanyoyin gudanar da sauye-sauye, da inganta moriyar albarkatun nahiyar, da ma zakulo hanyoyin da asusun zai bi wajen ci gaba da tallafawa tattalin arzikin nahiyar.

Lagarde ta kara da cewa, Afirka na da jan aiki a gaban ta, duba da irin gagarumar matsalar fatara da talauci da ta yi katutu a kasashen nahiyar, kari kan matsalar tattalin arzikin duniya da kawo yanzu ba a kai ga fita daga cikin ta ba baki daya.

Taron dai zai samu halartar mutane sama da 300, da suka hada da ministocin kudade, da gwamnonin bankunan kudin kasashen dake yankin. Kaza lika wakilan kasashe masu ruwa da tsaki a harkar hada-hadar cinikayya da nahiyar, daga kasashen Australia, da Brazil da Sin, za su halarci taron. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China