in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD ya nuna damuwa game da ayyukan Boko Haram
2015-02-03 14:47:24 cri

Kwamitin tsaron MDD ya fidda wata sanarwa, dake Allah wadai da karuwar hare-haren ta'addanci daga mayakan kungiyar Boko Haram, yana mai cewa, fitinar da mayakan kungiyar ke haddasawa a Najeriya da sauran kasashe makwaftanta, na barazana ga zaman lafiyar daukacin nahiyar Afirka.

Sanarwar ta bayyana harin baya bayan nan da mayakan suka kai, a yunkurinsu na shiga birnin Maiduguri, fadar gwamnatin Borno, da sauran hare-hare kan garuruwan dake yankin tafkin Chadi, a matsayin abin takaici.

Daga nan sai kwamitin tsaron ya jaddada kira ga mahukuntan yankunan da ke fuskantar barazana daga Boko Haram, da su hada gwiwa wajen daukar karin matakan murkushe kungiyar.

Bugu da kari kwamitin tsaron MDDr ya jaddada aniyarsa ta ci gaba da yaki, da dukkanin nau'o'in ayyukan ta'addanci, tare da gurfanar da masu aikata su gaban kuliya. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China