Dakaru wadanda ke biyayya ga janar Khalifa Haftar na sojan nan 'yan tawaye na kasar Libya sun kaddamar da wani sabon hari a ranar Lahadi, a kan sasanonin sojojin Islama a birnin Benghazi, wanda ke gabashin kasar. Wasu majiyoyi na cibiyoyin kiwon lafiya sun ce, harin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 4, da kuma raunata wasu mutane 9.
Kakakin Haftar ya ce, ana ci gaba da rangama da juna a bangaren yammacin bayan garin Benghazi, a cikin gundumar Sidi Faraj da al-Hawari, kamar yadda ya ce, fada ya kazanta domin sojoji 'yan tawaye na kai hari da tankokin yaki da rokoki a kan wasu da ya kira 'yan ta'adda.
Hakazalika dakarun Haftar sun kaddamar da hari ta jirgin sama, kamar dai yadda wasu da aka yi abin a kan idanunsu suka bayyan, sun ga jiragen yaki na ta zagaye sararin samaniyar Benghazi. (Suwaiba)