A ranar 12 ga wannan wata, hukumar kula da kiwon lafiya ta kasar Libya ta bayyana cewa, cikin 'yan kwanakin da suka gabata, sau tarin yawa mayakan sa kai da suke goyon bayan kungiyoyi daban daban na kasar suka yi kazamin fada tsakaninsu a garin Kikla da ke yammacin Tripoli, babban birnin kasar, inda a kalla mutane 21 suka rasa rayukansu, yayin da 60 suka ji rauni.
Wani kwamandan mayakan sa kai na Zintan wadanda ke goyon bayan kungiyar bin tunanin gargajiya ya bayyana cewa, a ranar 10 ga wata, mayakansu sun fara kai hari a garin Kikla mai tazarar kilomita 150 daga birnin Tripoli, wanda ke karkashin dakarun Fajr Libya mai goyon bayan kungiyar bin addinin musulunci.
Kwamandan ya ci gaba da cewa, dakarun Zintan sun riga sun mamaye garin Kikla a asubar ranar 11 ga wata, mazauna garin sun yi musu maraba sosai. Amma duk da haka, bangaren Fajr Libya ya musunta labarin, kuma ya bayyana cewa, dakarunsa sun riga sun murkushe harin da dakarun Zintan suka kai musu cikin nasara.
Bisa labarin da kamfanin dillancin labarai na Libya JANA ya bayar, an ce, mazauna wuraren da ke yammacin Tripoli da dama sun tsere daga muhallinsu domin gujewa hargitsin. (Jamila)