in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Kamaru sun ceto dan kasar Jamus daga hannun Boko Haram
2015-01-22 10:37:16 cri

A yayin wani samame da aka kai a cikin daren ranar Talata zuwa Laraba, rundunar jojojin kasar Kamaru ta ceto Nietzsche Herbert Hard Robert, wani bajamushen da kungiyar Boko Haram ta kasar Najeriya ta sace a cikin watan Yulin shekarar 2014, da kuma ci gaba da garkuwa da shi a cikin wannan kasa, in ji sakatare janar na fadar shugaban kasar Kamaru, Ferdinand Ngoh Ngoh.

Sojojin Kamaru sun gudanar da wannan samame tare da hadin gwiwar wasu kasashe, a cewar gwamnatin Yaounde. Shugaban kasar Kamaru, Paul Biya ya sanarwa 'yan kasa da duniya cewa, wani samamen musammun da sojojin Kamaru suke kai tare da hadin gwiwar wasu kasashe abokai ya taimaka wajen ceto Nietzsche Herbert Hard Robert, wani 'dan kasar Jamus, wanda kungiyar Boko Haram ta Najeriya ta sace a cikin watan Yulin shekarar 2014, kuma ta ci gaba da garkuwa da shi har zuwa wannan lokaci, a cewar mista Ferdinand Ngoh Ngoh a cikin wata sanarwa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China