in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Kamaru sun kashe mayakan Boko Haram fiye da 40
2014-12-29 09:54:57 cri

Rahotanni daga Yaounde, babban birnin kasar Kamaru sun nuna cewa, sojojin kasar sun yi nasarar hallaka fiye da mayakan kungiyar Boko Haram guda 40 a cikin wani taho mu gama da suke yi da juna a yankin nesa da arewacin kasar.

Kamar yadda ministan watsa labaran kasar Issa Tchiroma Bakary ya tabbatar a daren Lahadin, sai dai ya ce, daya daga cikin sojojin kasar ya rasa ransa a wannan gumurzu.

A bayanin da ya yi, mayakan sun kai hari ne a wurare da dama a yankin kwanakin baya da suka hada da Amchide, Limani, Makari, Chogori, Waza da Achigchia, duk wadanda ke kan iyaka da kasar Nigeriya.

Kafin nan, a safiyar Lahadin mayakan suka far ma Achigachia, abin da ya tilasta wa sojojin Kamarun ja da baya, daga baya kuma suka yi nasarar kwace garin bayan da sojojin samar suka kawo dauki da jiragen su.

Mayakan sun samu asarar mutanen su kwarai a Chogori, inda a nan kawai aka hallaka musu guda 34, in ji minista Issa Bakari. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China