in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Kamaru sun kashe mayakan Boko Haram fiye da 140
2015-01-13 10:06:13 cri

Aka kashe a kalla mayakan kungiyar Boko Haram 143 a cikin wani gumurzu tare da sojojin kasar Kamaru bayan sun yi yunkurin kai hari a wani sansanin soja a ranar Litinin da safe a Kolofata dake arewacin Kamaru, mai iyaka da Najeriya, a cewar ministan sadarwar kasar Kamaru, Issa Tchiroma Bakary a ranar Litinin da yamma.

A cewar ministan, daruruwan mayakan kungiyar Boko Haram sun yi dirar miki a safiyar Litinin da misalin karfe shida da rabi bisa agogon wurin a Kolofata, yankin dake kuriyar arewacin kasar Kamaru mai iyaka da Najeriya, sun kai hari da manyan makamai kan wani sansanin soja. Bayan sa'o'i biyar ana bata kashi, adadin mutanen da suka mutu ya tashi ga soji guda daga bangaren jami'an tsaro, kana 143 daga bangaren maharan, kuma wannan shi ne adadi mafi muni da Boko Haram ta samu tun farkon kai hare harenta da yin garkuwa da mutane a shekarar 2013, in ji minista Tchiroma Bakary.

A cewarsa, bayan samun nasarar murkushe mayakan Boko Haram, sojoji kuma sun karbe tarin makamai da kayayyakin sadarwa na zamani.

Yankin Kolofata ya taba fuskantar wani harin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane gomai a karshen watan Yuli, inda a yayinsa aka sace mutane kusan goma sha biyar, daga cikinsu kuma akwai matar mataimakin faraminista dake kula da hulda da 'yan majalisu, Amadou Ali, a cewar hukumomin kasar. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China