in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 3 sun rasa rayuka sakamakon harin Boko Haram a Kamaru
2015-01-19 09:44:02 cri

Rahotanni daga arewacin kasar Kamaru, na cewa, 'yan kungiyar Boko Haram sun hallaka mutane 3, tare da sace wasu yara 50, yayin wani farmaki da suka kaddamar kan wasu kauyukan yankin.

Baya ga asarar rayukan da harin ya haddasa, mahukuntan yankin sun ce, maharan sun kuma kone gidaje 80, suka kuma sace shanu 150 a harin na ranar Lahadi. Wata majiyar kamfanin dillancin labarun kasar Sin Xinhua, ta ce, maharan sun aukawa kauyen Tourou dake gundumar Mokolo mai iyaka da Najeriya, a daidai gabar da kasashen Kamaru da Chadi ke shirin hadin gwiwa na kawo karshen kungiyar ta Boko Haram.

Tuni dai tawagar farko ta dakarun sojin kasar Chadi ta isa Maroua, fadar mulkin yankin Arewa mai nisa na kasar Kamaru, domin fara aikin na hadin gwiwa.

Mayakan kungiyar Boko Haram dai na matsa kaimi wajen kaddamar da hare-hare a Kamaru, tun bayan harin Kolofata, na ran 12 ga watan Janairun nan, wanda a cewar mahukuntan kasar ya haddasa kisan mayakan su 143. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China