in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a rufe kotun TPIR a watan Satumba
2015-02-04 10:49:45 cri

Kotun hukunta manyan laifuffuka ta kasa da kasa game da kasar Rwanda (TPIR), dake da cibiya a birnin Arusha na kasar Tanzaniya, za ta dakatar da ayyukanta a cikin watan Satumba mai zuwa, bayan ta kwashe kusan shekaru ashirin tana gurfanar a gaban kotu wadanda ke da hannun tsamo tsamo a cikin kisan kiyashin shekarar 1994 a kasar Rwanda, yakin basasan da ya hallaka fararen hula kusan miliyan guda da ba su ji ba su gani ba.

Bisa shirye shiryen wannan rufewa, kotun ta sallami a baya bayan nan ma'aikatansa 117 daga 414, in ji jami'in TPIR mai kula da hulda da jama'a, Danford Mpumilwa a ranar Talata a cikin wata sanarwa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China