in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rwanda ta yi kiran da a dauki matakan soja kan 'yan tawayen FDLR
2015-01-04 09:52:01 cri

Gwamnatin kasar Rwanda ta yi kiran da a gaggauta daukar matakan soja kan 'yan tawayen FDLR da ke zaune a jamhuriyar demokiradiyar Congo.

Wannan kira ya zo ne ranar Jumma'a da dare sakamakon karewar wa'adin watanni shida da aka baiwa 'yan tawayen da su mika makamansu, ko kuma su fuskanci matakin soja.

Bugu da kari wannan shawara ta samu goyon bayan kwamitin sulhu na MDD, wanda ya umarci dakarun shiga tsakani na MDD da ke jamhuriyar demokirayar Congo da su farma 'yan tawayen.

Wata sanarwa da gwamnatin Rwanda ta bayar ta bayyana cewa, 'yan tawayen na FDLR sun yi amfani da wa'adin watanni shidan wajen kara karfinsu da nufin wargaza kasar, da ma yankin baki daya.

Don haka gwamnatin Rwanda ta nanata kiran da take ga gwamnatin jamhuriyar demokiradiyar Congo da tawagar MDD da ke Congo (MONUSCO) da su martaba nauyin da ke kansu a yankin, da ma kasa da kasa wajen ganin sun fatattaki 'yan tawayen.

A watan Yulin da ya gabata ne yayin taron ministocin harkokin wajen kasashen mambobin SADC da manyan tafkunan Great Lakes, aka baiwa 'yan tawayen na FDLR watanni 6 da su mika wuya ko su dandana kudarsu. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China