Wani kwamitin gwamnatin kasar Rwanda zai fara mahawara a bainar jama'a a ranar Laraba kan matsayin da gidan rediyo BBC ya taka wajen kisan kiyashin shekarar 1994 a kasar Rwanda, in ji majalisar dokokin kasar a ranar Litinin. Wannan kwamiti, da gwamnatin kasar ta kafa ba da jimawa ba, zai taimaka wa dukkan masu shaidu da su bayyana abubuwan da suka sani da suka taimaka wajen kara rura wutar gaba da ake zaton wannan kafar Burtaniya ta yada. Kwamitin dake kunshe da kwararru biyar a fannin ilimin 'yanci da sadarwa da kuma wasu wakilan kungiyoyin fararen hula, zai kasance a karkashin jagorancin tsohon babban alkalin kasar Rwanda Martin Ngoga. (Maman Ada)