Masu binciken laifuffuka a kasar Rwanda sun kammala bincikensu a kan shahararren mawakin nan Kizito Mihigo ta bukatar a mashi hukuncin rai da rai bisa laifin aikata ta'addanci da kisan kai.
Masu binciken kuma sun yanke wa tsohon 'dan jarida na tashar FM din Amazing Grace Radio, Cassien Ntamuhanga hukuncin. Mihigo ya shigar da neman ahuwa a kan zargin da ake masa, Ntamuhanga kuma ya ki amincewa da duk zargin da aka mashi.
Mutane biyu, ana tuhumar su ne tare da wadansu mutane biyu na daban wato Jean-Paul Dukuzumuremyi, wani soja da Agnes Niyibizi da duk suka musanta aikata laifuffukan da ake zargin su da su.
Mai binciken laifuffuka Boniface Budengeri Monday ya shaida wa babban kotun birnin Kigali cewa, wadanda ake zargin an same su da laifin hada kungiyar hada kai wajen adawa da gwamnati mai ci, ko shugaban kasa da kuma hannun su a ayyukan ta'addanci.
Mutanen har ila yau ana zargin su da shirin hallaka manyan jami'an gwamnatin Rwandan da dama, da jami'ai masu kayan sarki da hadin gwiwwa da jam'iyyar Rwandan National Congress, jam'iyyar adawa da aka dakatar da ita, da kuma jam'iyyar DFLR dake kasar jamhuriyar demokradiya ta Kongo. (Fatimah)