in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana cigaba da zanga-zangar nuna adawa da dokar zabe a DRC-Congo
2015-01-21 10:35:20 cri

Zanga-zangar nuna adawa da shirin dokar zabe, wanda ya kamata a tattauna batu a ranar jiya Talata a zauren 'yan majalisar dokoki, na cigaba da gudana a wasu yankunan birnin Kinshasa, hedkwatar kasar DRC-Congo, in ji wani wakilin Xinhua. A yankin Lemba, daliban jami'ar Kinshasa sun so fitowa kan tituna domin nuna rashin jin dadinsu, amma kuma jami'an kwantar da tarzoma da 'yan sanda kasar suka karya masu hanzari a cikin jami'ar. 'Yan sanda sun harba bindigogi domin tsoratarwa, amma ba za mu ja da baya ba, in ji wani dalibi, tare da bayyana cewa, a halin yanzu jami'ar ta rabu kashi biyu, bangare daya na jami'an tsaro, kana bangare guda na mu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China