Majalisar dokoki da majalisar dattawan kasar DRC-Congo sun amince a ranar Lahadi da kudurin dokar zabe da ba ta kunshe a yanzu da matakin dake tabbatar da yiyuwar zaben shugaban kasa mai zuwa bisa wani hurumin, sai an gudanar da wata kidayar al'ummar kasa. Zaben da aka yi a cikin majalisun biyu ya biyo bayan munanan zanga zanga da tashe tashen hankalin da suka barke a ranar Litinin da ta gabata a birnin Kinshasa, da suka janyo asarar rayukan jama'a da dukiyoyin jama'a da dama. (Maman Ada)