Kasashen Sin da Amurka sun dauki niyyar cimma matsaya mai alfanu kan sabane-sabanen dake tsakaninsu a yayin dandalin tattaunawar manyan batutuwa da tattalin arziki dake tsakanin kasashen biyu da aka kammala a ranar Alhamis a nan birnin Beijing.
Nasarar da aka cimma ta shawarwarin wannan zagaye na jaddada cewa, kasashen biyu na da karfi da sanin ya kamata wajen daidaita bambancin ra'ayinsu, da kuma sabane-sabanensu, in ji mataimakin faraministan kasar Sin Wang Yang, daya daga cikin shugabannin dandalin biyu na Sin, a yayin muhawarar rufe taron.
Mista Wang ya bayyana muhimmancin wannan dandalin tattalin arzikin da ya taimaka wajen cimma manyan batutuwan yarjejeniyoyi fiye da 90, dake aza tubalin shawarwari na gaba tsakanin shugabannin biyu da za'a shirya a cikin watan Nuwamba. (Maman Ada)