Bangarorin dake yaki da juna a kasar Sudan ta Kudu sun cimma ra'ayin gaggauta shirin zaman lafiya a cikin kasar, tare da nuna yabo game da taimakon da kasar Sin ta bayar wajen taimakawa kokarin shiga tsakani na kungiyar IGAD, a cewar wasu majiyoyin diplomasiyya a ranar Litinin.
A yayin wata tattaunawa tare da kungiyar IGAD da bangarori masu gaba da juna na kasar Sudan ta Kudu a karkashin jagorancin ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, bangarorin biyu dake gaba da juna a Sudan ta Kudu, sun cimma ra'ayin aiwatar bisa sahihanci yarjejeniyoyin da aka rattabawa hannu, da kuma kawo karshen tashe tashen hankali, a cewar wadannan majiyoyi.
Bangarorin biyu sun amince gaggauta shawarwari kan kafa gwamnatin wucin gadi, tare da daukar matakan da suka dace domin kyautata matsalar jin kai a yankunan dake fama da yaki, musammun ma wajen saukaka jigilar agajin jin kai na kasa da kasa.
Hakazalika bangarorin biyu sun dauki niyyar tabbatar da tsaron mutane da hukumomin kasashe daban daban dake kasar Sudan ta Kudu. Ta wani bangare kuma bangarorin sun jaddada goyon bayansu da himmatuwa ga kokarin kungiyar IGAD, da kuma nuna yabo kan goyon bayan da kasar Sin take baiwa gungun.
Mista Wang Yi ya shirya shawarwari domin ganin yadda za'a taimaka wa IGAD bunkasa hanyar sasantawa da gaggauta shimfida zaman lafiya da zaman karko a Sudan ta Kudu. (Maman Ada)