in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU za ta aike da jami'an sa ido a babban zaben Najeriya
2015-01-30 09:53:32 cri

Shugabar kwamitin hukumar gudanarwar kungiyar hadin kan Afirka uwargida Nkosazana Dlamini-Zuma, ta amince da tura jami'an sa ido Najeriya, domin nazartar yadda babban zaben kasar zai kasance.

Wata sanarwa da ofishin kungiyar ta AU ta fitar, ta ce, gabanin isar wakilan musamman da za su gudanar da takaitaccen aiki yayin zaben kasar, za a aiki da wata tawagar mutane 15, tawagar da za ta kasance a Najeriyar har ya zuwa ranar 11 ga watan Maris, domin nazartar daukacin sassan zaben baki daya.

Ana dai sa ran wannan tawaga, da kuma ta wakilan musamman su 50, za su gana da jami'an gwamnatin kasar, da na hukumar zabe, da 'yan takarar jam'iyyun siyasa, da wakilan kafofin watsa labarai, da kuma wakilan jam'iyyun gama kai.

Sanarwar ta kuma ce, aikin sanya idon da wakilan kungiyar ta AU za su gudanar, na da nufin tantance sahihancin zaben na watan Fabarairu, a wani mataki na tabbatar da kare tsarin dimokaradiyya, kamar yadda hakan ke kunshe cikin kundin mulkin Najeriyar, da ma sauran dokokin kasa da kasa.

Kaza lika rahotannin da wakilan AUn za su fitar, za su kunshi sakamakon da suka samu yayin aikin nasu, da kuma tsokaci, game da hanyoyin da suka dace a bi domin inganta zabukan kasar a nan gaba. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China