Kungiyar tarayyar Turai EU ta ce, ba za ta tura tawagarta ta masu sa ido kan zabukan Nigeriya zuwa yankin arewa maso gabashin kasar ba bisa dalilan tsaro.
Santiago Ayxela, shugaban tawagar sa idon na kungiyar wanda ya tabbatar da hakan a lokacin da ya ziyarci 'dan takara na jam'iyyar adawar kasar Janar Muhammadu Buhari a Abuja, babban birnin kasar ya ce, tawagar mai kunshe da jami'ai 90 tuni kashi na farko mai mutane 30 ya rigaya suka iso Nigeriya, kashi na biyu, inji Santiago Ayxela zai iso a ranar 7 ga watan Fabrairu, sannan kashi na uku zai so kafin ranar zaben.
A cewa Mr. Santiago Ayxela, zaben na Nigeriya yana da muhimmanci ga kasar, da kungiyar tarayyar Turai, da ma nahiyar Afrika baki daya, don haka duk abin da ya shafi Nigeriya zai shafi kungiyar tarayyar Turai da nahiyar Afrika.
Shugaban tawagar ya bayyana cewa, za su sa ido a kan shirin da kuma ayyukan masu ruwa da tsaki domin ganin an aiwatar da zaben bisa tsarin dokar kasar ba kawai a ranar zaben ba, har ma da kafin da kuma bayan zaben. (Fatimah)