Gwamnan jihar Adamawa dake arewa maso gabashin Najeriya Bala Ngilari, ya jaddada kira ga hukumar zaben kasar INEC, da ta dage zabukan dake tafe cikin wata mai zuwa a jihar.
Jihar Adamawa dai na cikin jihohin uku da hare-haren kungiyar Boko Haram suka fi shafa, wadda kuma ta dade karkashin dokar ta baci da gwamnatin tarayyar kasar ta kafa.
Bala Ngilari, ya ce, kiran nasa ya biyo bayan rahotannin sirri, da kuma hakikanin yanayin da jihar ke ciki a yanzu haka. Ya ce, a matsayinsa na wanda alhakin kare rayukan al'ummar jihar ya rataya a wuyansa, ba zai taba kallon wannan batu ta fuskar siyasa ba.
Gwamna Ngilari ya kuma bayyana takaicin yadda wannan bukata tasa, ta fuskanci suka daga 'yan siyasa, a yayin wani taron karawa juna sani da hukumar INEC ta shirya a kwanakin baya. Ya ce, yawancin masu sukar wannan bukata 'yan siysa ne da ke zaune a wajen jihar ta Adamawa. (Saminu)