Hukumar ba da agajin gaggawa a Najeriya NEMA, ta ce, ta yi rajistar mutane 5,000 a matsayin sabbin 'yan gudun hijira, sakamakon hare-haren da mayakan Boko Haram suka kaiwa garin Monguno, dake jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya.
Wata sanarwa da hukumar ta NEMA ta fitar, ta ce, harin na karshen mako ya yi sanadiyar rasa rayukan al'umma da dama. Baya ga gidaje da dukiyoyi masu yawa da mayakan suka barnata.
Sanarwar ta kara da cewa, yanzu haka NEMAn na amfani da wani ginin gwamnatin jihar ta Borno dake birnin Maiduguri, domin tsugunar da sabbin 'yan gudun hijirar. (Saminu)