in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kashe mayakan Boko Haram da dama a Najeriya
2015-01-26 10:10:07 cri

Rahotanni daga Nigeriya na bayyana cewa, sojojin kasar sun kashe mayakan Boko Haram da dama a ranar Lahadin nan lokacin da suka yi yunkurin afkawa cikin birnin Maiduguri da sauran garuruwan dake kusa na jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar.

Wani jami'in tsaro da ya tabbatar da hakan ga Xinhua ya kuma bukaci a sakaya sunan shi ya ce, mayakan Boko Haram suka kai hari a Maiduguri da sanyin safiyar Lahadi, sojojin kasar da aka jibge a wajen sun yi nasarar fin karfinsu, abin da ya sa da dama daga cikinsu aka kame saboda raunukan da aka ji musu, in ji majiyar.

Ya yi bayanin cewa, yanzu haka ana aiwatar da gaggarumin bincike bayan an killace harabar wajen duba a cikin wani kokarin da ake na tabbatar da yawan mayakan da hakan ya rutsa da su. Jami'in tsaron ya bayyana cewa, an kwace wata motar yaki, da manyan bindigogi da bindigogin masu sarrafa kansu da sauran makamai daga wajen mayakan da suka zubar don gujewa da ransu, ban da motoci kirar Gulf guda uku, makare da ababen fashewa da aka lalata su.

Wakilin Xinhua a Maiduguri ya ce, sojoji har ila yau sun yi nasarar fin karfin hare hare har sau biyu da aka kai a wannan ranar a garin Konduga. Ya ce, duk da cewa daga cikin sojojin, akwai wadanda suka mutu a jeren bata kashin da suka auku tsakanin su, sannan wadanda suka ji rauni, an tafi da su domin samar musu jinya.

Sai dai a cewar wakilin dake Maiduguri, komai ya lafa yanzu a garuruwan biyu, ana koma ci gaba da sintiri da motoci da kayayyakin bincike. Yanzu haka kuma an kafa dokar hana fita ta awannin 24 domin kammala bincike, ana fatan dage dokar in komai ya kammala. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China