Shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou, dake ziyarar aiki a yanzu haka a kasar Aljeriya, ya bayyana cewa, kasarsa da kasar Aljeriya sun cimma ra'ayi daya wajen hada karfinsu ta fuskar musanyar bayanai domin yaki da ta'addanci bisa fagen daga.
Mun cimma ra'ayi guda na tattara da hada karfinmu a fagen daga da musanyar bayanai domin kalubalantar barazanar ta'addanci da kungiyoyi masu dauke da makamai, in ji Mahamadou Issoufou a gaban manema labarai bayan wata ganawa tare da takwaransa na kasar Aljeriya Abdelaziz Bouteflika.
Da yake tabo dalilan wannan dangantaka, shugaban Nijar ja jaddada cewa, kasashen Aljeriya da Nijar, kasashe ne dake raba iyaka bisa kusan tsawon kilomita 1000, kuma suna da filayen hamada masu girma da ya kamata a kyautata tsaro cikin su. Maganar tsaro ta janyo yin musanya tsakanin tawagogin kasashen biyu, in ji shugaban kasar Nijar, musammun ma kan matsalar Libiya da Mali.
Game da huldar hadin gwiwa tsakanin kasarsa da Aljeriya, Mahamdou Issoufou ya ce, tana cikin yanayi mai kyau. Haka kuma za mu ba da wani sabon yunkuri ga dangantakarmu, in ji shugaba Issoufou tare da jaddada cewa, a nan gaba, dangantakarmu za ta kara samun sabon jini da fadada a fannonin tattalin arziki, siyasa, tsaro da zaman al'umma.
Bayan ricikin da ya barke a arewacin kasar Mali da lalacewar yanayin tsaro a kasar Libiya, kasar Nijar ta kasance daya daga cikin kasashe kalilan na shiyyar dake cin gajiyar dorewar siyasa cikin zaman lafiya. (Maman Ada)