in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban ofishin kiyaye zaman lafiya na MDD ya je Mali don karrama ma'aikatan da suka mutu
2014-10-08 09:58:08 cri

Shugaban ofishin kiyaye zaman lafiya na MDD Herve Ladsous yanzu haka yake a kasar Mali domin halartar bikin karrama ma'aikatan kiyaye zaman lafiya su 9, 'yan asalin kasar Nigeriya da aka kashe bayan da aka yi musu kwantar bauna makon da ya gabata.

Kamar yadda kakakin MDD Stephane Dujarric ya bayyana wa manema labarai a ranar Talatan nan, ya ce, Mr. Ladsous har ila yau yana Malin ne domin ya ba da kwarin gwiwwa ga ma'aikatan kasar Chadi wadanda su ma suka rasa nasu ma'aikatan a shegen wannan hadari makonnin da suka gabata.

A lokacin ziyarar, Herve Ladsous zai gana da shugaban kasar Mali Ibrahim Bubacar Kaita da kuma ministan harkokin wajen kasar.

Ma'aikatan kiyaye zaman lafiya su 9 daga Nigeriya, an yi musu kwantar bauna ne aka kashe su a ranar Jumma'ar da ta gabata a arewacin Mali, harin da ya fi muni ga ma'aikatan kiyaye zaman lafiya a kasar, in ji ofishin majalissar.

Kamar yadda bayani ya nuna dai, ma'aikatan sun gama da ajalinsu ne bayan da wadansu mutane da ba'a san ko su wane ne ba suka abka musu a kan hanyarsu a arewa maso gabashin kasar. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China