in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
ECOWAS za ta tura jami'an sa ido a zaben Najeriya
2015-01-22 09:57:58 cri

Kungiyar habaka tattalin arzikin yammacin Afirka ECOWAS, za ta tura jami'an sa ido a babban zaben Najeriya dake tafe cikin watan Fabarairun dake tafe.

Wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta nuna cewa, tsohon shugaban kasar Ghana John Kufuor ne zai jagoranci tawagar jami'an su 250.

Sanarwar ta ce, aikewa da wannan tawaga, na bisa tsarin yarjejeniyar shiyyar, wadda ta shafi bunkasa dimokaradiyya, da samar da sahihin jagoranci, da mambobin kungiyar suka amincewa.

Ana dai sa ran isar babbar tawagar Najeriya ne a ranar 10 ga watan Fabarairu, bayan isar tawagar musamman ta mutane 12, da za su nazarci sassan zaben daban daban, daga ranar 22 ga watan Janairu zuwa 18 ga watan Fabarairu.

Bisa tsarin aikin tawagar jami'an sa idon, babbar tawagar za ta mai da hankali ga lura da gudanar zaben, da kuma abubuwan da za su biyo bayan sa, yayin da tawagar musamman za ta tsara ayyukan gaggawa da za a iya bukata, ciki hadda ba da tallafin kare aukuwar rigingimu masu alaka da zaben. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China