Babban sakatare na MDD Ban Ki-moon ya bayyana damuwarsa a ranar Talata kan rikicin baya bayan nan a kasar Libya, musammun ma game da hare-hare ta sama kan biranen Tripoli da Benghazi da kuma kan tsaunukan Nafousa dake yammacin kasar.
A cikin wata sanarwa ta kakakinsa, mista Ban ya yi kira ga dukkan bangarorin da abin ya shafa da su kawo karshen kai hare-hare da kuma yin rigakafin duk wasu sabbin tashe-tashen hankali. Haka kuma ya tunatar da su bisa nauyin girmama imaninsu da doka domin kare fararen hula da girmama dokokin kasa da kasa kan 'yancin dan adam da 'yancin jin kai na kasa da kasa.
A cewar sanarwar, sakatare janar ya yi imanin cewa, hanya guda ta warware rikicin da ake fuskanta a halin yanzu ita ce hanyar yin shawarwari. Game da haka ya bayyana imaninsa kan aikin manzonsa na musammun, Bernardino Leon, da kokarinsa dake manufar saukaka yin shawarwari tsakanin 'yan kasar Libya domin tunkarar kalubalolin da kasar ke fuskanta, ta yadda za'a maido da tsarin demokaradiya, in ji sanarwar. (Maman Ada)