Mahukuntan kasashen Sudan da Chadi, sun bayyana gamsu game da yanayin tsaron kan iyakokinsu, nasarar da suka alakanta da managarcin aikin tsaro na hadin gwiwa da aka fara aiwatarwa tun a shekarar 2010.
A cewar ministan tsaron kasar Sudan Abdul-Rahim Mohamed Hussein, tun kafuwar rundunar tsaron hadin gwiwar kasashen biyu, ake ta kokarin lalubo hanyoyin warware matsalolin tsaro, dake addabar kan iyakokin kasashen, da ma batun dakile ayyukan 'yan tada kayar baya.
Hussein wanda ya bayyana hakan yayin taron ganawa da manema labaru na hadin gwiwa da takwaransa na kasar Chadi, a birnin Khartoum ya kara da cewa, rundunar ta kuma taimaka matuka, wajen karfafa kafuwar ayyukan ci gaba a yankunan dake kan iyakokin kasashen biyu, matakin da ya haifar da fa'ida mai tarin yawa ga al'ummun yankunan.
Wakilan kasashen biyu dai na ganawa ne a birnin Khartoum na Sudan, domin auna nasarorin da shirin tsaron hadin gwiwar nasu ya haifar.
Da yake tsokaci game da wannan batun, ministan tsaron kasar Chadi Benaindo Tatola, cewa ya yi, rundunar ta yi matukar ba da gudummawa, game da batun warware wasu muhimman lamurra da suka shafi kan iyakokin kasashen biyu. Rundunar ta hadin gwiwa dai na kunshe ne da sojoji 5,000 dake kunshe da rukunonin sojin 12 daga kasashen biyu. (Saminu)