in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yi kira da kawo karshen ginawa da lalatawa a Gaza
2014-10-22 14:58:59 cri

Babban sakatare na MDD, Ban Ki-moon, a yayin wani zaman taron kwamitin sulhu na MDD kan rikicin yankin Gabas ta Tsakiya, ya yi kira a ranar Talata da a kawo karshen zagayen ginawa da lalatawa a Gaza da ya sake faruwa a lokacin yakin da ya abku a wannan shekara. A cewarsa, ya kamata a dakatar da wannan yanayin ginawa da lalatawa. Ba za'a jiran a ko da yaushe ba gamayyar kasa da kasa ta rika karbar asarar wani sabon yaki da kuma biyan asara, in ji sakatare janar na MDD.

Albarkacin wannan dama, Ban Ki-moon ya yaba da sake maido da shawarwarin kai tsaye kan wani shirin dakatar da tsagaita wuta tsakanin Falesdinu da Isra'ila a karkashin jagorancin kasar Masar a birnin Alkahira.

Mista Ban ya nuna cewa, zaman lafiya cikin dogon lokaci na shiyyar na da nasaba da yarjejeniyar zaman lafiya daga dukkan fannoni, wadda za ta kai ga kafa wata kasar Falesdinu mai cike da zaman lafiya da 'yanci. Hanyar zaman lafiya ita ce hanya guda wajen cimma zaman lafiya mai dorewa. Lokaci ya zo na samu juriya da hangen nesa, ta yadda za'a cimma hanyar warware matsalolin da ke da sarkakiya tsakanin bangarorin biyu, a matsayin sakon da ya aike wa shugabannin Falesdinu da Isra'ila. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China