in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta bullo da shawarar ingiza zaman lafiya a Sudan ta Kudu
2015-01-13 14:09:01 cri

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya kawo wassu shawarwari guda hudu a ranar Litinin din nan, da zummar ingizar samar da zaman lafiya a kasar Sudan ta Kudu.

Mr. Wang ya kawo wadannan shawarwarin ne a wajen wani taron tattaunawa na musamman na kungiyar raya gwamnatocin gabashin Afirka IGAD a kan rikicin da ake fuskanta a kasar Sudan ta Kudu.

A lokacin taron, Mr. Wang ya bukaci bangarorin dake rikici da juna da su duba abin da zai amfani al'ummarsu na tsawon lokaci na gaba tare da kare zaman lafiya da kwanciyar hankalin yankin.

Ya ce, bangarorin biyu ya kamata su dakatar da amfani da karfin tuwo, su ci gaba ta hanyar rattaba hannu kan yarjejeniyar da za ta kai ga samun zaman lafiya ba tare da gindaye wassu sharudda ba, domin a samu yanayi mai kyau da za'a yi tattaunawa cikin lumana.

Haka kuma ministan harkokin wajen na kasar Sin ya bukaci a kafa gwamnatin rikon kwarya a kasar ba tare da bata lokaci ba, domin a gaggauta samar da zaman lafiya, yana mai kira ga iyakacin kokarin sauran kasashen duniya wajen ba da nasu taimakon samar da zaman lafiya, ci gaba da daidaito a kasar.

Wang Yi ya jaddada a cikin shawarwarin da ya gabatar cewa, kasar Sin tana goyon bayan kungiyar ta IGAD wajen taka rawar da ya kamata ta samar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu, ya kara da cewa, kasar ta Sin tana bin ra'ayin cewa, abin da ya shafi kasashen Afrika a bar nahiyar ta daidaita da kanta ta hanyar da suka ga ta kamace su.

Kasar Sin, in ji shi, za ta ci gaba da taimaka wa kungiyar IGAD tafiyar da harkokinta a bangaren kudi da kayan aiki. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China