in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kafa yankin kasuwanci cikin 'yanci na Afrika zai karfafa dangantakar kasuwanci tsakanin Sin da Afrika
2014-12-08 10:59:36 cri

Kafa wani yankin kasuwanci cikin 'yanci na Afrika bisa burin taimakawa musanyar kasuwanci a nahiyar a nan gaba zai kara bunkasa dangantakar tattalin arziki da kasuwanci tsakanin Sin da Afrika, in ji masanin tattalin arziki na kasar Benin Pascal Komlan a yayin wata hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a ranar Asabar.

Da farko, duk babu kafuwar wannan yankin kasuwanci cikin 'yanci na nahiyar, kasar Sin ta kasance cikin shekaru da dama, babbar abokiyar kasuwancin Afrika. Yanzu tare da kafuwar wannan sabon tsari, huldodin kasuwanci tsakanin Sin da Afrika za su karu fiye da yadda ake tsammani, in ji mista Komlan tare da jaddada cewa, kasuwanci tsakanin Sin da Afrika, na cigaba da karuwa tun fiye da shekaru da dama, inda ya cimma dalar Amurka biliyan dari biyu a shekarar 2013, idan aka kwatanta da na shekarar 2000 dake dalar Amurka biliyan goma.

Wannan yankin kasuwanci cikin 'yanci na Afrika ya kamata zai fara aiki nan da shekarar 2017, a cewar wannan masani. A ganin mista Komlan, wannan sabon tsarin kasuwanci, na yankin kasuwanci cikin 'yanci na Afrika, na daukar dunkulewar shiyyar a matsayin wani muhimmin mataki na shigar da kasashen Afrika cikin tattalin arzikin duniya. Kafuwar wannan yankin kasuwanci cikin 'yanci na Afrika zai kasance wata dama ga dukkan kasashen Afrika wajen gaggauta ajandarsu ta kawo sauyin tattalin arziki.

Burin wadannan kasashe, ba shi ba ne na tsaya cikin kasashe masu karamin karfi ba, amma gina wani tattalin arziki mai tasowa, in ji mista Komlan. Haka kuma ya jaddada cewa, shigowar kasar Sin a yawancin kasashen Afrika, musammun a wasu bangarorin gine gine, kamar gina hanyoyi na da muhimmancin gaske ga cigaban nahiyar da yawancin hanyoyinta suka lalace, har ma da kuma kawo sauki ga kasuwancin kayayyakin Afrika. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China