in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shirin cinikayya cikin yanci a Afirka zai daga matsayin hadin gwiwa da Sin
2014-11-28 10:30:58 cri

Masana a fannin tattalin arziki sun bayyana shirin da ake yi na kaddamar da sabon shirin gudanar da hada-hadar cinikayya cikin 'yanci, tsakanin manyan kungiyoyin nahiyar Afirka 3, a matsayin wani matakin da zai bunkasa hadin gwiwar Afirka da kasar Sin a fannin cinikayya.

Shi dai sabon shirin wanda ake sa ran kaddamar da shi cikin wata mai zuwa, zai kunshi hadakar kungiyar kasuwannin bai daya ta gabashi da kudancin Afirka ko COMESA a takaice, da kungiyar hadin kan gabashin Afirka ta EAC, da kuma ta bunkasa hadin kan kasashen kudancin Afirka ta SADC.

Kaza lika wannan shiri zai kunshi kasashe 26, wato kusan rabin adadin mambobin kungiyar AU ke nan, kasashen da ke kunshe da al'ummun da yawan su ya kai miliyan 625, kana ma'aunin GDPn su ya kai dalar Amurka tiriliyon 1.2. Kusan kimanin kaso 58 bisa dari ke nan na daukacin GDPn nahiyar baki daya.

A cewar Dr. Lubinda Habaazoka na jami'ar CBU, wannan shiri zai samar da dama ta kafa yankin cinikayya cikin 'yanci a nahiyar ta Afirka nan da shekarar 2017. Kaza lika zai ba da damar karfafa hadin gwiwar Afirka da Sin a fannonin cinikayya.

Shi ma a nasa tsokaci, Richard Musauka, shugaban ofishin hukumar samar da ci gaba ta kasa da kasa ko DPI reshen kasar Zambia, cewa ya yi shirin ya zo a daidai gabar da ake matukar bukatar sa, ganin yadda tuni kasar Sin ta gudanar da muhimman ayyukan raya kasa a kasashen Afirka da dama. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China