in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin ya yi kira da a goyi bayan Sahel wajen magance matsalar tsaro
2014-06-20 15:39:27 cri

Wani wakilin kasar Sin ya yi kira a kan kasashen duniya da su samar da tsayayyen goyon baya ga kasashen dake Sahel, domin magance matsalar tsaro dake addabar yankin.

Mataimakin zaunannen wakilin Sin dake MDD Wang Min, ya yi wannan kira ne a yayin da yake jawabi ga wani taron kwamitin tsaro na MDD a game da halin da ake ciki a yankin Sahel.

Wakilin na kasar Sin ya jaddada cewar, goyon bayan fafutukar kasashen yankin na Sahel, a kokarin su na samar da zaman lafiya mai dorewa, hakan shi ne zai samar da ingancin tsaro, da kuma magance halin da 'yan gudun hijira suka shiga yankin.

Wang Min ya gabatar da kira a kan kasashen duniya da su taimakawa yankin Sahel, ta hanyar hadin gwiwar a yankunan domin samar da horo a bangaren tsaro.

Mr. Wang ya bayyana cewar, kasar Sin tana girmama huldar dake tsakanin Sin da Afrika, domin Sin ta dade tana taimakawa kasashen Afrika.

Mr. Wang ya ce, Sin ta dade tana sa karfinta domin taimakon kasashen Afrika, domin yin gwaji a kan hanyar da ta dace da su, wacce za ta zaburar da tattalin arzikin kasashen na Afrika, a yayin da kasashen ke neman hadin kan kasashensu, tare da samun karfin gwiwa na nemo hanyoyin da za su kai su ga cimma bunkasa, tare da samar wa kansu mafita a kan al'amurran yankunansu, wanda ya hada da matsalar yankin na Sahel.

Ya kara da cewa, a nan gaba, kasar Sin za ta inganta huldarta da kungiyoyi na duniya da na yankuna, ciki har da MDD, a kokarin da take yi na ba da gagarumar guddumuwa ta magance matsalolin Sahel, tare da zaburar da zaman lafiya da ci gaba mai dorewa a Afrika. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China