Sojojin Nigeriya a jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar sun tabbabar da hallaka mayakan Boko Haram 78 a lokacin wata arangama da suka yi bayan da mayakan suka yi kokarin shiga garin Biu.
Wata majiyar tsaro mai tushe ta shaida wa Xinhua cewa, da sanyin safiyar Laraba ne lamarin ya faru, a cikin wadanda aka hallaka, har da wassu 'yan kasashen waje, sannan an damke wasunsu, a kalla an kirga gawawwaki 78 na mayakan, in ji wannan majiya.
Ya ce, an samu manyan bindigogin harbar jiragen sama guda biyu daga hannun mayakan a lokacin arangamar. Yana mai bayanin cewa, an yi dauki ba dadi sosai tsakanin sojojin Nigeriya da wadannan mayakan kafin su samu kwato ikon jihohin Adamawa, Borno da kuma Yobe daga hannun mayakan wadanda suka yi kaka gida. (Fatimah)