Kaftin din kungiyar wasan kwallon kafa ta Cote d'Ivoire wadanda aka fi
sani da giwaye watau elephants, Yaya Toure ya ce, ya yi farin ciki matuka a yayin da suka yi kunnen doki a wasanta da suka buga da kasar Guinea, a karkashin rukunin D, a wasan kwallon kafa na gwagwarmayar lashe kofin Afrika AFCON, wanda ake ci gaba da yi a kasar Equatorial Guinea dake Afrika ta yamma.
Giwayen na Kwadebuwa sun yi gumuzu sosai da 'wasan kwallon kafa na kasar Guinea, kuma har sai da aka fitar da 'dan wasansu guda a zagaye na biyu na wasan kuma sun yi ta kai hari domin zura kwallo a gidan 'yan wasan kasar Guinea, to a karshe dai an kammala wasan da 1 da 1 a filin wasan kwallon kafa na Malabo.
Kaftin din 'yan wasan na kasar kwadebuwa ya ce, sun buga kwallo da tawagar kwararrun 'yan wasan kwallo na kasar Guinea, to amma a karshe ya ce, ya yi farin ciki sun yi canjaras. (suwaiba)