in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'ar MDD ta yi kiran inganta hadin kai domin tunkarar kalubale dake addabar Sahel
2014-06-20 10:48:02 cri

Manzon musamman ta MDD a kan batun yankin Sahel, ta shaidawa kwamitin tsaro na MDD jiya Alhamis ranar 19 ga wata cewar, kasashen dake yankin Sahel a Afrika, suna ci gaba da fafutuka domin magance matsalolin siyasa da na tsaro wadanda ke fuskantar yankin, ta kuma bukaci karin hadin gwiwa na kasashen yankin, makwabta da kuma kasashen ketare wadanda Afrikar ke aiki da su.

Guebre Sellassie, cikin jawabinta na farko ga kwamitin tsaron na MDD, ta ce, tabarbarewar al'amurran siyasa da tsaro a yankin da wasu wurare kusa da yankin, wani abu ne mai hadarin gaske, musamman kasancewar kungiyoyin 'yan ta'adda a Nigeria da gabashin Afrika.

Sellasie ta ci gaba da cewar, MDD na kokarin tsara wani shiri da zai karfafa matakan tsaro da gwamnatocin kasashen da abin ya shafa, a karkashin wani mataki na MDD, wadda ta bullo da shi shekarar bara domin taimakawa yankin.

Ta bukaci kasashen duniya da su ci gaba da taimakawa domin haka ta cimma ruwa. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China